A wannan gari mai suna Lajamanu dake jahar Northern Territory kimanin kilomita 560 kudu ta yamma(wato southwest) da garin katherine dake kusa da Hamada mai suna Tanami, abin al’ajabi mai girma da ya auku a cikin daren lahadin da ta gabata dai, ana alakanta shi da wani babbar iko ne na ubangiji Subhanahu wata’ala.
A wannan gari wanda ya ke nesa da cikin biranai, a yayin wani dan biki na hasashen yanayi da aka aiwatar cikin daren lahadi ne dai, Allah ya aiko musu da ruwa tare da kifi masu rai daga sama. Ku kalli video a kasa.
A cewar wani mazaunin garin mai suna Andrew Johnson Japanangka Lajamanu, wanda Kanisila ne a wannan garin.
Mun ga wani hadiri mai girma ya garkamo, a tunanin mu ruwa ne kawai za’a yi kamar kullum. A yayinda ruwan ke zubowa, kawai sai mukaga kifaye na zuba da ransu. Kifayen da suka zubo kanana ne girmansu kamar yatsu biyu
Andrew Johnson Japanangka Lajamanu
Wannan dai ba shi ne na farko ba da hakan ke faruwa a kasar Australia. A shekarar 2016, Irin hakan ya faru a wani karamin kauye mai suna Winton da ke Jahar Queensland. Hakan ya biyo bayan fama da fari da matsanin rashin ruwa na wani lokaci.
Masana ilimin yanayi dai suna hasashen cewa hakan kan iya faruwa ne sakamakon guguwa mai karfi a kusa da wadannan garuruwa . Guguwar takan iya debo wadannan kifaye daga ruwa sannan tayi sama da su sosai . A yayin da su ke zubo wa lokacin zubar ruwan sama. A cewar Dr Unmack
Hakan na iya faru a daidaikun lokuta , A yayin da iska ko guguwa mai karfi ke diban kifaye daga teku zuwa sama sosai, gabani kuma su zubo cikin ruwa.
Dr unmack
labari daga nzherald