An kori wasu iyalai ‘yan garin Detroit na Amurka daga jirkin sama bayan fasinjoji sunyi korafi kan warin jikinsu.
Mutumin mai suna Yossi Adler, matarsa mai suna Jennie da ‘yarsu suna hanyarsu ne na dawo wa gida daga yawon jin dadi a daren laraba daga garin Miami na Amurka. Amma kafin jirkin su ta tashi, An kira jami’ai sun firda su tare da raka su waje zuwa kofar Airport na Miami.
‘Kwatsam, bayan sun fitar damu daga jirgin sai suka rufe gate sannan suka ce “Sai hakuri bawan allah, wadansu sun yi korafin warin jikin ka saboda haka bazamu barka ka koma cikin jirgi ba” ‘
Yossi Adler ya fada wa kafafen labarai
‘Jikin mu baya wari , ba mu da wani matsala
inji Adler
Adler ya yi amfani da wayar sa ya dau bidiyon sa da matarsa a lokacin da abin ya faru kuma suke magana da ma’aikatan jirgi.
Ya ce ‘Ba mu da warin jiki, ba wani mai warin jiki anan’
Da aka tuntubesu, American Airlines sun tabbatar da korar Adler daga jirgin bayan mafiyawan fasinjoji sun yi korafi kan warin jikinsa.
Kamfanin jirkin suka kara da cewa sun bawa iyalan dakin hotel, da takardan abinci kauta har zuwa safiyar alhamis
Adler ya kara da cewa kamfanin jirgin kuma tayi alkawarin sauke masa kayar sa da ya riga ya shigar cikin jirgi wadanda suka hada da kujerar zama na yara da babbar jakansa, amma kamfanin bata yi hakan ba. An tafi da kayan nasu zuwa detroit bayan su an sauke su a airport na Miami. Iyalan sun karbi kayan su ne kadai bayan sun isa jida daga baya.
Matar mutumin wato Jennie tace sun roki mutane da dama a airport din su shinshina su sannan su fada musu ko da gaske ne suna wari
‘Abin da kunya amma haka mu ka tambaya “Shin ko muna wari don allah, ku shinshina mu ku fada mana domin an fitar da mu daga jirgi saboda wari”. Jama’a sukan taya mu alhinin abin tare da cewa “Mai yasa kamfanin ta muku haka?” ‘
Inji Jennie, matar Adler
Adler yana zargin da akwai wani dalili daban da yasa aka kore su. Shi yana so kamfanin ta fadi gaskiya kawai mai makon karya.