Birnin mai suna “Forest city” wato birnin daji kenan da hausa wani kokari ne na wata kanfanin China wanda ta yi don ta gina wurin zama da rayuwa cikin nishadi ga mutane sama da miliyan daya amma kash abin dai bai yiwu ba!
Kamfanin dai ta kashe akalla sama da dalar Amurka billion dari(100) don gini da kammala birnin wanda yake a bakin teku a wani jaha mai suna Johor Bahru dake kasar Malaysia. Shi wannan birni dai ya kunshi kayatattun wuraren nishadi da suka hada da wurin sayayya, babbar kasuwa(wato super market), jadawalin wasan kallo na golf, wajen wasa da ruwa(wato water park) da kuma kyatattun gidajen cin abinci.
An fara gina birnin ne a shekarar 2016, amma labarin da manema labarai suka ruwaito ya numa cewa kashi 15 cikin 100 ne kadai a ka kammala ginawa na birnin, kuma hasali ma kashi daya a cikin dari ne na birnin mutane ke ciki. Wannan lamari ya sa birnin ya zamo tamkar kufayi shekara da shekaru duk da kuwa kudaden da aka kashe wurin gina shi.
A yanzu dai wasu su na kiran wannan birni da suna “Ghost town”, wato kufayi kenan da hausa.
Duk da cewa shi kamfanin na kasar China mai suna Country Garden daya gina wannan wuri yana sa ran cewa zai samu damar kammala ginin kuma har ma jama’a su shiga kamar yanda ya yi niyya a baya, amma a zahiri dai shi wannan kamfani yana cikin tsaka mai wuya saboda makudan kudaden da akebin sa kimanin dalar Amurka biliyon 200. Wannan lamari shi yasa mutane da yawa ke ganin kammala wannan babbar birni dai bazai yiwu ba, hasali ma asara kawai aka tafka na gina wannan wuri.
Abin tambaya dake zukatan jama’a dai shine, shin mai yasa har wayau jama’a basu shiga sashin wurin da aka gama ba ?
Gidan labarai na BBC ya ruwaito cewa shi wannan birnin dai an gidan shine da niyyar sayarwa da yan kasar China da gidaje a kasar Malaysia .Hasali ma dai kudin da aka tsula wa gidajen yafi karfin mafiya yawar yan asalin kasar Malaysia sai dai bakin kasar China wanda dama don su aka gina birnin.
Masu nazari sun yi kokarin gano dalilin ci bayar wannan birni, wasu daga cikin sanadin da aka gano dai sun hada da cutar COVID. Zuwa cutar covid ko kuma Corona shima ya taimaka wajen da kile wannan birni. Abu na biyu da yafi kowanne girma kuma shi ne takunkumi da shugaban kasar China wato Xi ya saka na hana fitar da kudi daga kasar zuwa waje shima ya kawo chikas.
Yanzu haka dai wasu mazauna birnin da kuma kamfanin da ta gina wurin suna ta kokarin gyara sunan birnin amma hakan dai ya ci tura.