A wata sha shida kadai, Muhammad Kenzi Alfaro yana da nauyin 60lbs , wanda hakan ke nuna yafi dan shekara takwas nauyi . Kuma akan sa masa nafkin size XXXL wanda manya zasu iya sawa.
Bidiyon yaron dai wanda aka dauka a gidansu dake yankin Bandung na kasar Indonesia , ya ba jama’a mamaki.
A mafi yawa, yara sa’oinsa nauyin su kan kai 22lbs, amma shi wanna jariri ya nika hakan sau uku. .
Mahaifiyarsa mai suna Pitriah girmansa yayi yawa, ko abin tura yara(wato baby stroller) bai iya daukansa. Kibar ta sa kuma wanna yaro bai iya tsayiwa ko zama da kansa sai an dauke shi.A cewar mahaifiyar sa:
Mahaifinsa bai da jiki, saboda haka kayan mahaifinsa ma yana masa daidai. Kuma wataran kayar mahaifinsa muke sa masa. Kuma nafkin da muke saya basa iya rike shi. dole sai cikin dare kadai ake iya sa masa nafkin. kuna nafikin mafi girma ma basu iya masa daidai sai an matsa sosai. Nafkin in da zai iya daukansa wato XXXL suna wahala A garinmu, hasali ma ba kullum muke samu ba.
Patriah , Mahaifyar Jariri Muhammad
Tun farko dai shi Muhammad Kenzi an haifeshi da girma, nauyinsa yakai 10lbs a haihuwa. Amma wannan nauyi dai ya kara tunzura tuni .
Masu kiwon lafiya sukan kai ziyara gidan su kuma su duba shi domin kula da lafiyarsa a kullum. A halin yanzu dai a na ma wannan jariri gwaji a wani asibiti mai suna Hermina Bekasi Hospital domin kokarin gani yanda za’ayi ya rage kiba.
A halin yanzu dai ba’a san dalilin da kibar Muhammad yayi yawa ba. Ministan lafiya mai suna Budi Gunadi Sadikin yace ya bada ma’aikatar kiwon lafiya umurnin su kula da wannan jariri kuma su rinka bashi update na abinda ke faruwa game da hakan.