Wasu dalibai a china sun kirkiri na’urar sumbatar juna bai dogon zango
Wasu dalibai a china sun kawo mafita ga masoya wadanda basu zaune wuri daya ta hanyar kirkirar na’urar sumbata bai dogon zango. Ita wanna na’ura dai takan bada masoya damar sumbatar juna daga nesa , kuma suji kamar suna tare. Amma wayar sanarwar dai, wanna na’ura da yayi amfani da fasaha na 3D don siffanta lebba ya jawo cecekuce sosai a yanar gizo
Shi wannan fasahar dai an wallafa shi a Changzhou Vocational Institute of Mechatronic Technology a yankin Jiangsu dake gabashin China. Nau’rar anyi shi ne da silicon material kuma yana da baki irin ba mutum sak wanda aka yi shi da laushi tare da fata na silicon. An yi shi ne da siffar baki na dan Adam don a koikoyikoyi, motsi tare da dumi na lebbar mutum ta hanyar amfani da sensors da ke jikin na’urar.
Shi na’urar yana aiki ne ta hanyar hada shi da mobile app , sannan a sanya shi a cajin port. Bayan mutum ya pairing da masoyi ko masoyiyarsa ne dai , masoyan biyu zasu uploading kiss insu ta bakin na’urar. Shi kuma daga bisani zai dauki sautin muryarsu a yayin wannan kiss sannan a isar wa masoyinsu ta dayan zangon.
Shi dai engineer wanda ya kirkiri na’urar mai suna Jiang Zhongli ya fada wa Global Times cewa a lokacin da ya kirki ri na’urar dai suna zaune a gari dabam da basoyarsa. Hasali ma, kewar nata shi yasa shi hakan.
A lokacin ina jami’a, ina soyayya da masoyiya ta ne daga gari mai nisa , saboda haka bama samun ganin juna sai dai magana ta waya. hakan ya sani kirkirar wannan na’ura.
Jiang Zhongli
Remote kissing device for long-distance lovers, invented and patented by Chinese university student in Changzhou City.
— China in Pictures (@tongbingxue) February 22, 2023
The mouth-shaped module, served as an inducing area for lovers to make the kiss and then it can transfer kiss gesture to the “mouth” on the other side. pic.twitter.com/5i2ogMiUXe
A halin yanzu dai ana saida wannan naurar a katafaren sashin saye da sayarwa na China wato Taobao a misalin dala 38.
Daga Independent